Karamar Hukumar Gwarzo Ta Bukaci Sabbin Malanai su riƙe ka’idojin aikin.

Daga Khadijah Aliyu

Kano Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta bukaci malaman da aka dauka aiki na firamare su kiyaye ƙa’idojin aiki da suka hada da zuwa aiki akan lokaci da zuwa aiki akai-akai da jajircewa da kuma gaskiya wajen gudanar da ayyukansu.

Sakataren Ilimi na Ƙaramar Hukumar Gwarzo, Malam Ashiru Lawan Kutama, ne ya yi wannan kira a cikin wata sanarwa da ya fitar a Kano.

Ya bayyana cewa shirye-shirye sun yi nisa na karɓar aiki ga sabbin malaman da aka ɗauka aiki ƙarƙashin BESDA.

Kutama ya bayyana cewa za a gudanar da shirin wayar da kan malamai ne ranar Asabar, 5 ga Satumba, 2026, a Model Primary, Gwarzo, daga ƙarfe 9:00 na safe.

Ya shawarci dukkan malaman da suka sama aikin su halarci shirin tare da zuwa da takardun amincewa tare dana ɗaukar aiki waɗanda za su kasance cikin takardun da ake buƙata yayin gudanar da aikin.

A cewarsa, an tsara shirin ne domin ba wa sabbin malaman ilimi da fahimtar da ake buƙata domin su gudanar da ayyukansu na koyarwa yadda ya kamata.

Ya ce za a ilmantar da malaman game da ayyukansu da haƙƙoƙinsu a matsayin malamai, da kuma hanyoyin gudanar da aiki da ƙa’idojin da ake nema tare dasu na tafiyar da harkokin ilimi.

Kutama ya yi kira ga malaman da su nuna ƙwazo da jajircewa da sadaukarwa wajen gudanar da ayyukansu, ya kuma jaddada muhimmiyar rawar da suke takawa wajen inganta harkar ilimi a Ƙaramar Hukumar Gwarzo da Jihar Kano baki ɗaya.

 

Fassara Hauwa Muhammad Lawal

You May Also Like

Fire Service Rescues Man, Cow from Well in Kano

The Kano State Fire Service has rescued a 40-year-old man and his…

Hadejia-Jama’are Authority Reclaims 600,000 Hectares of Farmland in Kano

By KHADIJAH ALIYU The Hadejia-Jama’are River Basin Development Authority says it has…

NBAIS Registrar Traces Institution’s Legacy to Sardauna’s 1960 Vision

Writing By Umar S Fada; Editing By Yusuf Zubairu  The Registrar of…

2027 Hajj: IHR Urges NAHCON, States, Tour Operators To Revamp Pilgrims’

  By Adamu Yusuf The Independent Hajj Reporters (IHR) has called on…

Tarauni Volunteers Intensify Drainage Clearing Against Flooding

By Khadijah Aliyu  Volunteer groups across the 10 wards of Tarauni Local…

FG Urges States To Domesticate Inclusive Education Policies

By Shindong Bala     The Federal Government has urged state governments…
Download FRCN Kaduna Hausa App