Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, na cikin jerin manyan jami’an da aka zaba su raka Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a wata muhimmiyar ziyarar aiki ta ƙasa zuwa Birtaniya, wadda ake kallon ta a matsayin ziyarar tarihi tsakanin ƙasashen biyu.

 

Shugaban Ƙasa tare da Uwargidansa da sauran ’yan tawagarsa za su tashi daga Abuja ranar Talata domin fara wannan ziyara ta musamman.

 

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana cewa Sarkin Birtaniya, King Charles III, zai karbi baƙuncin Shugaba Tinubu, Uwargidansa da tawagarsu a fadar sarauta ta Windsor Castle daga ranar Laraba 18 ga Maris zuwa Alhamis 19 ga Maris, 2026.

 

Sanarwar ta bayyana cewa manufar ziyarar ita ce ƙara danƙon alaƙa tsakanin Nijeriya da Birtaniya tare da duba hanyoyin haɗin gwiwa a fannoni kamar kula da shige da fice, kasuwanci, zuba jari da mu’amalar al’adu.

 

Haka kuma, za a gayyaci Shugaban ƙasa da tawagarsa domin duba wani baje kolin kayan tarihi na sarauta da suka shafi Nijeriya, yayin da iyalan sarauta za su shirya liyafar girmamawa ga baƙin.

 

A yayin ziyarar, Shugaba Tinubu zai gana da Firaministan Birtaniya, Keir Starmer, domin tattauna batutuwan haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu, wanda ake sa ran zai kai ga rattaba hannu kan yarjejeniyoyi a fannoni kamar kasuwanci, zuba jari, tsaro da musayar al’adu.

 

Haka kuma, Shugaban ƙasa zai halarci wani baje kolin fasaha na zamani mai taken “Nigerian Modernism,” tare da ganawa da manyan ‘yan kasuwa na Nijeriya da Birtaniya da kuma ‘yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje.

 

Ana sa ran wannan haɗuwa za ta ƙara buɗe ƙofar zuba jari da hulɗa ta tattalin arziki.

 

Sanarwar ta ƙara da cewa, kasancewar Gwamna Dauda Lawal cikin tawagar zai ba shi damar ƙulla sabbin alaƙa da masu zuba jari da hukumomi, lamarin da zai iya jawo muhimman damar ci gaban tattalin arziki ga Jihar Zamfara.

Aminu Dalhatu

Demboss Data App
You May Also Like

Jigawa APC Congress Peaceful, Namadi Urges Party Discipline

Governor Malam Umar Namadi has commended the peaceful and successful conduct of…

APC Membership Hits 158,697 in Zamfara After Gov Lawal’s Defection

The Secretary to the Zamfara State Government SSG, Malam Abubakar Mohammad Nakwada,…

Gov Lawal Dumps Opposition, Joins APC Following Consultations

The Governor of Zamfara State, Dauda Lawal, has officially defected from the…

All Progressives Congress Elects New State Executives in Kano 

Writing by Abdullahi Jalaluddeen Editing by Abubakar Hamza.     All Progressives…